<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Lokacin da ka ke shan wahala fa,
 Lokacin da Shaiɗan ya ke damunka,
 Tuna da alherin Ubangiji inka,
 Wannan dai zai ba ka karfin zuciya.

[V2]
 KORUS
 Har matuka Yesu yana nan
 Har matuka Yesu yana nan
 Har matuka Yesu yana nan
 Shi ba zai rabu da kai ba, ko kaɗan.

[V3]
 2) Sa'ad da ka duba masu dukiya,
 Tuna da alkawarin Mai Cetonka,
 Rai madauwami ne shi ya ce zai bayar
 Ga duk wanda ya ke ba da gaskiya.
 Korus

[V4]
 3) Idan ka gaji da halin duniya,
 Kana neman rabuwa da ruɗinta,
 In ji Ubangiji, &quot;Ina jiranka,
 Zo, ka karƃi hutawa a wurina.&quot;
 Korus

[V5]
 4) Ko a matse ka ke, babu fasawa,
 Shaiɗan yana neman ƃata halinka,
 Sai ka ta da murya ga Allahnmu,
 Shi ba za ya yarda ba ka lalace .
 Korus</lyrics>
<title>Lokacin da Ka Ke Shan Wahala Fa LW206</title>
<hymn_number>206</hymn_number>
</song>